Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yakin da kasar Sin ke yi da annobar cutar numfashi ta COVID-19
2020-03-01 16:00:51        cri
Kasar Sin ta dauki matakai iri daban daban da nufin dakile cutar numfashi ta COVID-19 da ta barke. Ga sabbin nasarori na baya bayan nan da aka cimma kawo yanzu.

Ya zuwa ranar Asabar, kasar Sin ta samu rahoton sabbin mutane 573 da suka kamu da cutar yayin da mutane 35 suka mutu a duk fadin kasar a sanadiyyar cutar.

A ranar ta Asabar mutane 2,623 aka sallama daga asibiti bayan sun warke daga cutar, kamar yadda hukumar lafiyar kasar ta bayyana.

Baki dayan mutanen da suka kamu da cutar a duk fadin kasar Sin ya kai 79,824 ya zuwa ranar Asabar, wanda ya kunshi majinyata 35,329 da ake kula da lafiyarsu, sannan mutane 41,625 aka sallama daga asibiti bayan sun warke daga cutar, kana mutane 2,870 cutar ta hallaka a kasar.

Hukumar lafiyar kasar Sin ta kara da cewa, akwai mutane 851 da ake tsammanin sun harbu da kwayar cutar.

Mataimakiyar firaministan kasar Sin Sun Chunlan ta yi kira a ranar Asabar cewa ya kamata a dauki kwararan matakan bincike domin gano tushen kwayar cutar, da irin salon da take yaduwa, da yadda ake magance cutar, da yadda ake tantance magungunan cutar da kuma cigaban da aka samu a aikin samar da alluran riga kafin cutar, kana da dora muhimmanci waje yin amfani da magungunan gargajiyar kasar Sin wajen warkar da majinyatan da suka kamu da kwayar cutar.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China