Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwajin cutar COVID 19 da aka yi wa mutane 11 da ake zargin sun kamu a Nijeriya ya nuna ba su da ita
2020-02-28 09:53:11        cri
Cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta Nijeriya NCDC, ta ce gwajin cutar COVID-19 da aka yi wa jimilar mutane 11 da ake zargin sun kamu da cutar a kasar, ya nuna ba su da ita.

Shugaban hukumar NCDC, Chikwe Ihekweazu, wanda ya tabbatarwa manema labarai hakan a Abuja, babban birnin kasar, ya kuma tabbatarwa 'yan kasar samun kariya daga cutar, biyo bayan jita-jitar da ake yadawa cewa an tabbatar da bullar cutar a jihar Lagos, cibiyar harkokin kasuwanci ta kasar.

A cewarsa, dakunan gwaji 4 dake kasar, na da karfin gwada cutar COVID-19, yana mai cewa, suna karkashin cibiyar, kuma suna aiki ba dare ba rana.

Ya kara da cewa, suna tuntubar ma'aikatar lafiya ta jihar Lagos da na sauran jihohi, kuma za a sanar da al'umma, da zarar an tabbatar da bullar cutar a Nijeriya. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China