Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO: COVID-19 ta tsananta a wajen kasar Sin
2020-02-28 12:12:19        cri
Babban darektan hukumar lafiya ta duniya (WHO) Adhanom Gybereyesus, ya bayyana a jiya Alhamis cewa, duniya ta shiga wani muhimmin lokaci, na yakar annobar COVID-19, yayin da sabbin wadanda suka kamu da cutar a wajen kasar Sin ya dara adadin wadanda suka kamu da cutar a cikin kasar.

Jami'in na WHO ya bayyana cewa, batun muhimmin lokaci da ya ambata kan cutar, na nufin abin da ke faruwa a wajen kasar Sin da kuma cikin kasar. Yana mai cewa, alamu na nuna cewa, idan har aka dauki managartan matakai kamar yadda kasar Sin ta yi, hakika za a samu raguwar wadanda ke kamuwa da cutar har daga karshe a shawo kan ta baki daya.

Ya ce, a daya hannun kuma, karuwar wadanda ke kamuwa da cutar a wasu sassan duniya, musamman kasashen Iran da Italiya da Koriya ta kudu, ba labari ne mai dadin ji ba.

Don haka, ya yi gargadin cewa, idan aka hada wadannan bangarori biyu, hakan na nuna cewa, duniya na cikin wani yanayi mai hadari, kuma cutar na iya bazuwa ta ko'ina, gwargwadon matakan da muka dauka.

Darektan na WHO ya kara yin kira ga dukkan kasashe, da su gaggauta daukar managartan matakai, don hana yaduwar cutar kafin kwayar cutar ta gagari kwandila.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China