Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta kalubalanci Amurka da ta girmama kaidojin kasuwa
2019-12-27 13:23:04        cri

Kwanan baya, kasar Amurka ta tanaji dokar kasafin kudinta ta ayyukan soji na shekarar 2020, inda aka sanya wasu miyagun matakai masu nasaba da masana'antun kasar Sin.

Dangane da haka, kakakin ma'aikatar kasuwancin kasar Sin Gao Feng, ya bayyana jiya cewa, kasar Sin ta ki yarda da hakan, tana kuma fatan Amurka za ta dakatar da matakinta, a kokarin samar da kyakkyawan yanayi na yin hadin gwiwa a tsakanin masana'antun kasashen 2 ta fuskar tattalin arziki da ciniki.

A yayin taron manema labaru da aka saba shiryawa a nan Beijing, Gao Feng ya nuna cewa, kasar Sin na ganin cewa, wasu matakan da ke cikin tanajin dokar, sun saba wa kalaman da Amurka ta sha yi, wato yin ciniki cikin adalci da 'yanci, za su keta odar kasa da kasa ta fuskar tattalin arziki da ciniki, kana za su illata tsarin masana'antun duniya. Kasar Sin ta kalubalanci Amurka da ta girmama ka'idojin kasuwa, ta daina kallon duniya bisa tunaninta a fannin siyasa, da yin watsi da tunanin cin moriya da faduwar wani. Ta dakatar da kallon kasar Sin bisa tunaninta, da matakan na kuskure, a kokarin samar da kyakkyawan yanayi na yin hadin gwiwa a tsakanin masana'antun kasashen 2, ta fuskar tattalin arziki da ciniki (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China