Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin da Amurka za su kulla yarjejeniyar tattalin arziki da cinikayya ta matakin farko a mako mai zuwa
2020-01-09 16:20:13        cri
Yau Alhamis, kakakin ma'aikatar kasuwancin kasar Sin Gao Feng ya bayyana a birnin Beijing cewa, kasar Sin da kasar Amurka, za su kulla yarjejeniyar tattalin arziki da cinikayya ta matakin farko a mako mai zuwa.

Gao Feng ya ce, bisa gayyatar da kasar Amurka ta yi wa kasar Sin, wakilin ofishin siyasa na kwamitin tsakiyar JKS, kuma mataimakin firaministan kasar Sin, kana jagoran shawarwarin tattalin arziki dake tsakanin kasar Sin da kasar Amurka Liu He, zai kai ziyarar aiki a birnin Washington DC daga ranar 13 zuwa ranar 15 ga wata, domin kulla yarjejeniyar tattalin arziki da cinikayya ta matakin farko.

A halin yanzu kuma, bangarorin biyu suna tattaunawa kan jadawalin kulla yarjejeniyar. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China