Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan sabbin mutanen da suka warke daga cutar COVID-19 ya ninka yawan wadanda suka kamu da cutar a kwanaki 9 a jere
2020-02-27 10:46:34        cri

Hukumar lafiyar kasar Sin ta sanar a yau cewa, yawan sabbin mutanen da suka warke daga cutar numfashi ta COVID-19 a kasar Sin ya ninka yawan sabbin mutanen da suka kamu da cutar a cikin kwanaki 9 a jere.

A ranar Laraba mutane 2,750 aka sallama daga asibiti bayan sun warke daga cutar, adadin ya ninka yawan sabbin mutanen da suka kamu da cutar a wannan rana, wato mutane 433.

Baki daya mutane 32,495 aka sallama daga asibiti bayan sun warke daga cutar ya zuwa ranar Laraba, a cewar hukumar lafiyar.

Ranar Laraba ita ce rana ta takwas wacce aka samu adadin mutane kasa da 1,000 da suka kamu da annobar cutar numfashi ta COVID-19 a fadin kasar Sin.

Ya zuwa ranar Larabar, mutane 78,497 ne aka tabbatar sun kamu da cutar numfashi ta COVID-19 a kasar Sin daga larduna 31 na kasar Sin, baki daya mutane 2,744 cutar ta hallaka a fadin kasar.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China