Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta ba da rahoton sabbin mutane 2,015 da suka kamu da cutar numfashi
2020-02-12 12:51:23        cri

Hukumar kiwon lafiyar kasar Sin ta fitar rahoto cewa, a jiya Talata 11 ga wata, akwai sabbin mutane 2,015 da aka tabbatar sun kamu da cutar numfashi, kana an sallami mutane 744 daga asibiti bayan sun warke daga cutar, kana wasu mutane 97 sun mutu sanadiyar cutar.

Haka kuma, an sami rahoton sabbin mutane 377 da aka tabbatar sun kamu da cutar numfashi a wasu sassan kasar ban da lardin Hubei, adadin da ya ci gaba da raguwa cikin kwanaki 8 da suka gabata.

Ya zuwa jiyaTalata, baki dayan yawan mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar a babban yankin kasar Sin sun kai 44,653, sa'an nan, an salami mutane 4,740 daga asibiti bayan sun warke daga cutar, kana mutane 1,113 sun mutu sanadiyyar cutar. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China