Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Hukumomi sun dauki matakan kandagarki da dama a yankunan karkara
2020-02-12 11:39:19        cri

Rahotanni daga taron manema labarai na tsarin hadin gwiwar ayyukan kandagarki da hana yaduwar cuta na majalisar gudanarwar kasar Sin da aka kira a jiya Talata a birnin Beijing na cewa, babban burin aiwatar da aikin kandagarkin cutar corona a yakunan karkara shi ne "hana shigowar kwayoyin cutar numfashi daga waje, da hana yaduwar cutar numfashi". Haka kuma, hukumar kiwon lafiyar kasar Sin za ta gaggauta aikin samar da kayayyakin kandagarki ga yankunan karkarar kasar Sin, kana, jami'in ma'aikatar kula da aikin gona da raya yankunan karkara ya yi kira ga bangarori daban daban na Sin da su hada kai don taimakawa yankunan karkara ta fuskar ayyukan kandagarki.

Mataimakin darektan sashen ba da jagoranci kan hadin gwiwar tattalin arzikin yankunan karkara Mao Dezhi ya bayyana cewa, hukumomi a yankunan karkara sun bukaci mazauna kauyuka da su daina ziyartar gidajen abokai, da shirya taruka, sa'an nan kuma, sun yi rajistar dukkanin mutanen da suka dawo kauyankansu daga wasu wurare, su kuma bincike lafiyarsu yadda yakamata. A sa'i daya kuma, su rika fadakar da jama'a game da matakan kandagarki, ta yadda al'ummomin kauyuka za su fahimci muhimmanci na yin kandagarki.

Sashen kula da harkokin kiwon lafiyar fararen hula na kwamitin kiwon lafiyar kasar Sin Nie Chunlei ya bayyana cewa, hukumomin da abin ya shafa suna daidaita ayyukan samar da kudade da kayayyaki ga yankunan karkara, an kuma dawo da harajin yuan 5 da aka sanyawa ko wane mutum na kasar Sin ta fuskar kiwon lafiya ga dukkanin unguwannin dake birane da kauyuka, wanda za a yi amfani da kudin wajen yin kandagarki kan cutar numfashi. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China