Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan sabbin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19 ya kai 508
2020-02-25 12:31:11        cri

Bisa labarin da hukumar kiwon lafiya ta kasar Sin ta bayar a yau, yawan sabbin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar numfashi ta COVID-19 a kasar Sin a ranar 24 ga wannan wata ya kai 508, yawan sabbin mutanen da suka mutu a sakamakon cutar a wannan rana ya kai 71, kana yawan sabbin mutanen da aka sallama daga asibiti bayan sun warke daga cutar ya kai 2589.

Ya zuwa ranar 24 ga wannan wata, bisa rahoton da larduna da birane da yankuna 31 suka gabatar, yawan mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar numfashi ta COVID-19 a kasar Sin ya kai 47672, yawan mutanen da suka warke daga cutar ya kai 27323, kuma yawan mutanen da suka mutu a sakamakon cutar ya kai 2663, gaba daya adadin dukkan mutanen da aka tabbatar da sun kamu da cutar ya kai 77658. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China