2020-02-18 11:49:51 cri |
Yayin taron manema labaran da aka yi a jiya Litinin, jami'in hukumar kiwon lafiyar kasar Sin ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu, an riga an tura ma'aikatan likitanci sama da dubu 32, daga babban yankin kasar Sin zuwa birnin Wuhan na lardin Hubei, kuma galibinsu, ma'aikatan likitanci a fannonin numfashi ne, da cututtuka masu yaduwa da kuma cututtuka masu tsanani, an kuma tura tawagogin nas-nas da dama zuwa wurin.
Bisa labarin da aka samu, an ce, an fi tura ma'aikatan likitanci na fannonin cututtuka masu tsanani zuwa birnin Wuhan, inda adadinsu ya kai dubu 11, wanda ya kasance 10% cikin dukkanin ma'aikatan likitanci na fannonin cututtuka masu tsanani a duk fadin kasar Sin, sabo da an fi samun mutanen dake kamuwa da cutar masu tsanani a wannan birni. A halin yanzu, an fidda daftarin ba da jinya ga masu kamuwa da cutar numfashi ta COVID-19 karo na shida, domin ba da jagoranci ga dukkanin ma'aikatan likitancin kasar Sin, da kuma kyautata ayyukansu.
Ban da haka kuma, hukumomin lafiya sun sanya tawagogin ba da jinya na gaggawa guda 22, da dakunan gwajin likitanci na P3 guda uku, da kuma wasu ma'aikatan bincike, da su ba da taimako ga birnin Wuhan da ma lardin Hubei baki daya. (Maryam)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China