![]() |
|
2020-02-08 17:16:23 cri |
Hukumar kiwon lafiya ta kasar Sin, ta tabbatar a yau Asabar cewa, ta karbi rahoton sabbin wadanda suka kamu da cutar Corona 3,399 yayin da wasu 86 suka mutu, daga larduna 31 da jihar Xinjiang na kasar a Juma'a.
Hukumar ta kara da cewa, a jiya Juma'a, an sallami mutane 510 daga asibiti bayan sun warke.
Jimilar wadanda suka kamu da cutar a babban yankin kasar Sin ta kai 34,546 ya zuwa jiya Juma'a, inda kuma jimilar wadanda suka mutu sanadiyyar cutar ya kai 722. Baya ga haka, an salami jimilar mutane 2,050 daga asibiti bayan sun warke. (Fa'iza Mustapha)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China