Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masanin Amurka: Kokarin Sin na yaki da cutar COVID-19 ya burge duniya sosai
2020-02-25 14:10:33        cri

A kwanakin baya, farfesa W. Ian Lipkin na cibiyar nazarin cututtuka na kwalejin kiwon lafiyar jama'a a jami'ar Columbia ta kasar Amurka ya koma kasar Amurka inda ya yi hira da wakilin babban gidan rediyo da telebijin na kasar Sin wato CMG cewa, kokarin kasar Sin na yaki da cutar numfashi ta COVID-19 ya burge duniya sosai. Ana kiran Lipkin da sunan kwararren kashe kwayar cuta, wanda ya taba zuwa kasar Sin a karshen watan Janairu don taimaka wajen yaki da cutar COVID-19. Ya yi kira ga jama'a da su maida hankali kan labaru game da cutar daga bangaren gwamnati da hukumomi, kuma kada a yi imani da jita-jita. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China