Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Dole ne Amurka ta dakatar da tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar Sin ta hanyar fakewa da batun addini
2020-02-26 20:51:24        cri

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya bayyana a yau Laraba a nan birnin Beijing cewa, sau da dama, wasu Amurkawa na fakewa da batun addini don yada jita-jita, da nufin tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar Sin, wanda hakan ke yunkurin illata hadin kan al'ummomin Sinawa baki daya, kuma ya sanya Sin nuna matukar rashin jin dadin ta.

An ba da labarin cewa, jakada mai kula da 'yancin addinai na majalisar gudanarwa ta kasar Amurka Sam Brownback, ya ce Sin na daukar muggun matakai na sauya halayyar musulmi mazauna kasar ta Sin ta yadda ala tilas za su zama masu biyayya ga kasar, kuma hakan shi ma wani nau'i ne na yaki da masu bin addinai.

Yayin da yake amsa tambayoyin da aka gabatar masa dangane da wannan batu, a gun taron manema labarai da aka gudanar, Zhao Lijian ya ce gwamnatin kasar Sin na kokarin kiyaye hakkin mazauna kasar na bin addinai cikin 'yanci bisa doka, kuma kowane mutum na iya zabar addinin da yake son bi.

A cewarsa, jihar Xinjiang na da masallatai dubu 24.4, wanda hakan ke bayyana cewa, duk musulmai 530 na da masallaci guda na ibada, amma adadin masallatan da ke akwai a Amurka, bai ma kai kashi 10 cikin dari bisa na kasar Sin ba.

Ya ce na yi gargadi ga wannan jakada, da ya dakatar da fakewa da batun addini, yana yin shisshigi a harkokin cikin gidan kasar Sin. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China