Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ba za ta dakatar da zirga-zirgar jiragen sama na fasinja ba
2020-02-06 19:11:01        cri

Hua Chunying, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bayyana ta kafar Intanet yau Alhamis cewa, kasar Sin ta dauki wasu matakan da suka dace kan zirga-zirgar jiragen sama na fasinja, a kokarin kiyaye lafiyar fasinjoji na ketare, da kuma hana yaduwar annobar cutar numfashi ta hanyar jirgin sama. Hua Chunying ta tabbatar da cewa, kasar Sin ba za ta dakatar da zirga-zirgar jiragen sama na fasinja ba.

Hua Chunying ta fadi haka ne yayin da take mayar da martani kan shawarar da wasu jami'an kasashen waje suka baiwa al'ummominsu da ke zaune a kasar Sin da su bar kasar cikin hanzari. Inda suka nuna damuwa cewa, mai yiyuwa ne kasar Sin za ta dakatar da zirga-zirgar jiragen sama na fasinja nan da wasu makonni masu zuwa. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China