Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jacob Mudenda: Zimbabwe za ta yi hadin kai da kasar Sin wajen tinkarar cutar numfashi ta COVID-19
2020-02-21 13:52:58        cri

Shugaban majalisar wakilan kasar Zimbabwe Jacob Mudenda, ya shaidawa manema labarai cewa, Zimbabwe na tsayawa tare da kasar Sin, wajen goyon bayan kokarin kasar na tinkarar cutar numfashi ta COVID-19.

Ya ce, yana farin ciki sosai bisa ganin ci gaban da Sin ta samu a wannan fanni. A cewarsa, yana jinjinawa sosai ga matakan da gwamnatin Sin ke dauka a yaki da wannan annoba da ta barke ba zato ba tsamani, kuma kasarsa ma na da imanin cewa, Sin za ta samu nasara.

Jacob Mudenda ya yi wannan tsokaci ne, bayan ganawar sa da jadakan Sin dake Zimbabwe Guo Shaochun. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China