Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Hukumomi a Zimbabwe na bincike kan kwararar sabbin takardun kudi a kasuwar bayan fage
2019-11-15 11:01:18        cri

Babban bankin Zimbabwe RBZ, da hukumar yaki da cin hanci ta kasar, na bincike kan kwararar sabbin takardun kudi a kasuwar bayan fage, bayan har yanzu wasu kwastomomin bankin ba su kai ga samu ba.

A ranar Litinin ne bankin ya saki sabbin takardun kudi na dalar Zimbabwe 2 da 5, domin saukaka karancin tsabar kudi da ake fuskanta a kasar, inda jama'a suka fara samun kudin a ranar Talata, sai dai adadin ba yawa, la'akari da bankuna sun kayyade yawan kudin da mutum zai samu wanda ya tsaya tsakanin dalar Zimbabwe 40 zuwa 100.

Sai dai, hotunan makudan sabbin kudaden da aka fitar wajen bankunan na yawo a kafafen sada zumunta, lamarin da ya sa bankin RBZ da sauran masu ruwa da tsaki daukar mataki.

Ma'aikatar yada labarai da wayar da kai ta kasar ta wallafa jiya a shafinta na Twitter cewa, gwamnatin ta fara bincike kan batun ta hannun bankin na RBZ.

Ma'aikatar ta ce bankuna sun karbi tsabar kudin ne ta hanyar amfani da motocin jigilar kudi a ranar Litinin. Kuma an ajiye dukkan lambobin dake jikin kudin. Don haka za a bayyana sunayen bankunan da suka keta doka tare da hukunta su. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China