Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An gama aiki na mataki na biyu na gina asibitin sada zumunta a tsakanin Sin da Zimbabwe
2019-11-17 16:52:18        cri

A jiya ne, aka gudanar da bikin kammala aiki na mataki na biyu na ginin asibitin sada zumunta na Mahusekwa a yankin Mahusekwa dake jihar gabashin Mashonaland ta kasar Zimbabwe.

Shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa ya halarci bikin tare da bude asibitin a hukumance. Shugaba Mnangagwa ya nuna godiya ga gwamnatin kasar Sin domin ta samar da gudummawa ga kasarsa, ya ce, wannan asibiti ya zama alamar shaida zumunta a tsakanin Sin da Zimbabwe, a cikin shekaru da dama da suka gabata, Sin ta gina manyan ayyukan more rayuwa da dama a kasar Zimbabwe, kana ta gudanar da ayyukan dake shafar rayuwar jama'a a fannonin aikin noma, da bada ilmi, da kimiyya da fasaha, da kiwon lafiya da sauransu, wanda ya sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arziki da zamantakewar al'ummar kasar.

A nasa bangare, jakadan Sin dake kasar Zimbabwe Guo Shaochun ya bayyana a gun bikin cewa, Sin da Zimbabwe sun sada zumunta a dogon lokaci, da yin hadin gwiwa da juna a fannoni daban daban. A shekarar bara, an inganta dangantakar dake tsakanin kasashen biyu zuwa dangantakar abokantaka ta hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare, a nan gaba kasashen biyu za su ci gaba da zurfafa hadin gwiwarsu a dukkan fannoni don kara amfanawa jama'arsu. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China