Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaba mnangagua na Zimbabwe ya gana da Wang Yi
2020-01-13 21:12:51        cri
A yau Litinin ne shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagua, ya gana da dan majalissar gudanarwa, kuma ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, a birnin Harare fadar mulkin kasar Zimbabwe.

Yayin zantawarsu, Mr Mnamgagwa, ya ce yayin da ake tsaka da gudanar da ayyukan 'yantar da kasa, da kare muradun cin gashin kan kasa, da nuna kyamar tsoma hannun kasashen yammacin duniya, da takunkumin da suke kakabawa Zimbabwe, kullum Sin ta kasance mai nuna goyon baya ga kasar, matakin da a cewarsa Zimbabwen ba za ta taba mantawa da shi ba.

Shugaba Mnamgagwa ya ce, Zimbabwe na jinjinawa Sin, bisa tallafin ta a fannin bunkasa tattalin arzikin Zimbabwe, da ma sauran sassan na inganta zamantakewar al'ummar kasar. Ya ce yana fatan Sin za ta ci gaba da taimakawa Zimbabwe, wajen gaggauta aiwatar da sauye sauyen tattalin arziki, da cimma manyan nasarori a wannan fanni.

A cewar sa, Zimbabwe na nacewa ga manufar nan ta kasar Sin daya tak a duniya, da ma sauran batutuwa da suka shafi muhimman manufofi da Sin din ke maida hankali a kan su.

A nasa bangare kuwa, Mr. Wang Yi bayyana goyon bayan Sin ya yi, ga kokarin Zimbabwe na kare 'yancin mulkin kai, da kare muradun cin gashin kai, da kimar kasar ta Zimbabwe, da ma martaba hanyar da kasar ta zaba, ta wanzar da ci gaban kan ta. Ya ce Sin na da burin ganin an dagewa Zimbabwe takunkumai marasa adalci, ba tare da bata wani lokaci ba. Kaza lika Sin na da burin ganin Zimbabwe ta fadada kawance, da hadin gwiwa da karin kasashe, ta kuma bunkasa musaya da sauran sassan duniya.

Daga nan sai ya godewa Zimbabwe, bisa goyon baya maras iyaka da take nunawa, ga batutuwa da suka jibanci muhimman manufofin Sin. Ya ce Sin za ta samar da karin taimako da goyon baya ga Zimbabwe gwargwadon iyawarta, za ta kuma raba fasahohin da take samu, ta fuskar kwarewar jagoranci da Zimbabwe. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China