Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Babban bankin Zimbabwe ya ce yana samun kwarin gwiwa a shirinsa na dena taammali da dala
2020-02-18 10:42:58        cri

A ranar Litinin babban bankin kasar Zimbabwe ya sanar cewa yana samun kwarin gwiwa tun bayan kaddamar da shirinsa na dena amfani da nau'ikan kudaden kasashen waje a kasar wanda ya kaddamar da shirin a watan Yunin bara.

Gwamnan babban bankin kasar Zimbabwe John Mangudya, ya ce za'a dauki tsawon shekaru biyar kafin kasar ta samu nasarar kammala shirin dena amfani da kudaden, ya ce a halin yanzu an samu nasarar rage ta'ammali da kudaden waje a kasar daga kashi 50 zuwa kashi 37 bisa 100 ya zuwa ranar 31 ga watan Disambar 2019.

Gwamnan ya gabatar da tsarin bayanan tsarin manufofin kudaden kasar na shekarar 2020.

Mangudya yace babban bankin kasar yayi amanna cewa shirin bunkasa tattalin arzikin kasar wanda ya kunshi tsara manufofin kudin kasar, da kokarin samar da makoma mai kyau ga cigaban tattalin arzikin kasar, da takaita hawa hawar farashin kayayyaki suna samun kyautatuwa wajen taimakawa shirin dena amfani da kudaden waje a kasar sannu a hankali, wanda aka kuduri aniyar cimmawa nan da shekaru biyar masu zuwa. Wannan shirin yayi daidai da yadda wasu kasashen duniya suka aiwatar kuma suka samu nasara.

A watan Yunin bara kasar Zimbabwe ta haramta amfani da kudaden kasashen waje kimanin tara, wanda suka hada har da dalar Amurka wacce ta mamaye harkokin hada hada a kasar tun a shekarar 2009, kana an sake gabatar da yin amfani da kudi na dalar kasar Zimbabwe wanda aka yi watsi da shi tun a shekarar 2009. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China