Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wang Yi: Sin da Zimbabwe za su kasance aminai har abada
2020-01-13 10:35:02        cri
Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kana minista mai kula da harkokin wajen kasar, Wang Yi, tare da minista mai kula da harkokin diflomasiyya da ciniki tsakanin kasa da kasa na kasar Zimbabwe Sibusiso Moyo, sun kira taron manema labaru a jiya, bayan ganawar da suka yi, a birnin Harare, hedkwatar kasar Zimbabwe, inda mista Wang Yi ya bayyana sakamakon da suka cimma yayin ganawar, wadanda suka hada da:

Na farko, Sin da Zimbabwe suna da zumunci mai karfi. kuma Kasar Sin na son zama aminiyar kasar Zimbabwe har abada.

Sa'an nan, na biyu, akwai makoma mai haske ga hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Zimbabwe. Ya ce Kasar Sin na sane da cewa, Zimbabwe na fuskantar wasu matsaloli, kuma bisa matsayinta na aminiyar kasar, a shirye Sin take, ta gabatar da dabaru da shawarwari, ta yadda za a samu karin damammkin raya tattalin arziki da zamantakewar al'ummar kasar.

Haka zalika, a bangare na 3, kasashen 2 za su iya taka muhimmiyar rawa a kokarin daidaita al'amuran duniya. Ya ce yayin da ake neman warware wasu matsaloli, kasashen Sin da Zimbabwe za su nace ga ra'ayin tabbatar da adalci, tare da kokarin tabbatar da moriyar bai daya ta kasashen dake tasowa. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China