Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mataimakin shugaban kasar Zimbabwe ya gana da ministan harkokin wajen kasar Sin
2020-01-13 16:20:26        cri
A jiya Lahadi, mataimakin shugaban kasar Zimbabwe, Constantino Chiwenga, ya gana da mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kana ministan harkokin wajen kasar, mista Wang Yi, a Harare, hedkwatar kasar Zimbabwe.

A wajen ganawarsu, Chiwenga ya ce bangaren Zimbabwe na son ganin karin kamfanonin kasar Sin sun zuba jari a Zimbabwe. Sa'an nan gwamnatin kasar za ta yi kokarin kyautata muhallin kasuwanci, da saukakawa 'yan kasuwa ayyukansu.

A nasa bangare, Wang Yi ya ce, kasar Sin za ta kasance aminiyar kasar Zimbabwe har abada. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China