Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jakadan Sin: Shugabannin kasashe sama da 160 sun nuna goyon bayan su ga kwazon Sin na shawo kan cutar COVID-19
2020-02-21 10:40:06        cri
Jakadan kasar Sin a ofishin MDD dake birnin Geneva Chen Xu, ya ce Shugabannin kasashe sama da 160, da jagororin hukumomin kasa da kasa 30, sun nuna goyon bayan su ga kwazon Sin, na shawo kan cutar numfashi ta COVID-19.

Chen Xu, wanda ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da ya gudana a jiya Alhamis, ya ce matakan Sin na kandagarki da shawo kan cutar, baya ga kare lafiyar jama'ar Sinawa, suna kuma baiwa sauran sassan duniya damar shirya tunkarar wannan annoba.

Ya ce tawagar hadin gwiwa ta Sin, da kwararru na hukumar lafiya ta duniya WHO, suna kara matsa kaimin gudanar da ayyuka, kuma Sin za ta gabatar da dabarun kandagarki, da na shawo kan wannan cuta, domin al'ummar ta da ma sauran sassan duniya baki daya.

A ranar 18 ga watan Fabarairun nan ne, mujallar kasa da kasa ta Lancet ta ayyukan likitanci ta wallafa wata makala mai taken "jawabin goyon bayan masana kimiyya, kwararrun ma'aikatan lafiya, da masana magunguna bisa aikin Sin na yaki da cutar COVID-19".

Rahotanni sun nuna cewa, manyan masana harkokin lafiya na kasa da kasa 27 daga kasashe 8 ne suka sanya hannu kan wannan jawabi, wanda kuma kasar Sin ta jinjinawa. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China