Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO: Sin na aiwatar da matakai mafiya dacewa a yakin da take yi da cutar COVID-19
2020-02-19 12:26:15        cri
Babban darakta mai lura da sashen ayyukan gaggawa na hukumar lafiyar ta duniya WHO Dr. Michael Ryan, ya ce matakan da kasar Sin ke aiwatarwa a yanzu haka, su ne mafiya dacewa, a yakin da take yi da cutar numfashi ta COVID-19. Ya ce WHO na fatan ganin karin ci gaba, a aikin kula da lafiyar al'umma da Sin ke aiwatarwa.

Dr. Ryan, ya ce makwanni da yawa da Sin ta kwashe tana yaki tukuru da wannan cuta, ta hanyar sanya ido har a matakai na gida-gida, ya haifar da raguwar adadin wadanda suke kamuwa da ita a baya-bayan nan.

Jami'in ya kara da cewa, matakin farko a Wuhan, shi ne tsayar da cutar a tushen ta, wanda hakan zai ba da damar sanya ido kan ta, kuma ta hakan ne za a dakile yaduwar ta ga sauran masu lafiya. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China