Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Asibitocin Sin sun sallami wadanda suka warke daga cutar numfashi ta COVID-19 su 14,376
2020-02-19 10:26:49        cri
Hukumar kula da lafiyar al'umma ta kasar Sin, ta ce ya zuwa karshen ranar Talata, adadin wadanda suka warke daga cutar numfashi ta COVID-19, aka kuma sallame su daga asibiti sun kai mutum 14,376. Kana a ranar Talatar kadai, an sallami mutane 1,824 daga asibiti, bayan da aka tabbatar sun warke daga cutar.

A daya hannun kuma, ya zuwa karshen ranar ta Talatar, adadin wadanda cutar ta hallaka ya kai mutum 2,004, yayin da jimillar mutane 74,185 suka kamu da ita, a yankunan lardunan kasar 31 da yankin aikin soji na Xinjiang. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China