Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta tabbatar da sabbin mutane 1749 sun kamu da cutar ta COVID-19 yayin da wasu 136 suka mutu
2020-02-19 10:27:42        cri
Hukumar lafiya ta kasar Sin ta ce ta samu rahoton cewa, ya zuwa jiya Talata, sabbin mutane 1749 sun kamu da cutar numfashi ta COVID-19, yayin da sabbin wadanda suka mutu suka kai 136, daga larduna 31 na kasar da Jihar Xinjiang.

Daga cikin wadanda suka mutu, an samu 132 ne a lardin Hubei, yayin da aka samu daddaya a lardunan Heilongjiang da Shandong da Guangdong da Guizhou. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China