Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan mutanen da suka kamu da cutar COVID-19 a wajen Hubei ya ragu cikin kwanaki 10 a jere
2020-02-14 13:45:34        cri
Hukumar kula da lafiya ta kasar Sin ta sanar cewa adadin sabbin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar numfashi ta coronavirus (COVID-19) a wajen lardin Hubei, inda annobar cutar ta fi kamari, yana matukar raguwa a cikin kwanaki 10 a jere.

Baki daya yawan sabbin mutanen da aka tabbatar da sun kamu da cutar a wajen Hubei a ranar Alhamis kimanin 267 ne, a cewar kididdigar da hukumar ta fitar a yau Juma'a.

Hukumomin lafiyar kasar Sin sun sanar a yau Juma'a cewa sun samu rahoton sabbin mutane 5,090 da aka tabbatar sun kamu da annobar cutar numfashi ta novel coronavirus, da yawan sabbin mutanen da suka mutu 121 a ranar Alhamis daga cikin larduna 31 da yankin sojoji na Xinjiang.

Hukumomin lafiyar kasar ta Sin sun sanar cewa kimanin majinyata 6,723 aka sallama daga asibiti bayan sun warke daga cutar numfashin ya zuwa ranar Alhamis.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China