Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta samu sabbin majinyatan da suka warke daga cutar COVID-19 fiye da yawan wadanda suka kamu da cutar a karon farko
2020-02-19 13:24:14        cri
A karon farko kasar Sin ta samu sabbin majinyatan da suka warke daga annobar cutar numfashi ta COVID-19 da suka zarce yawan sabbin mutanen da suka kamu da cutar, hukumar lafiyar kasar ce ta sanar da hakan.

Alkaluman da hukumar lafiyar kasar ta sanar a yau Laraba ya nuna cewa, a ranar Talatar da ta gabata an samu kimanin majinyata 1,824 da aka sallama daga asibiti bayan sun warke daga cutar, adadin da ya zarce yawan sabbin mutanen da suka kamu da cutar numfashin ta COVID-19 a wannan rana wato mutane 1,749.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China