Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan sabbin masu kamuwa da cutar COVID-19 a wajen Hubei ya ragu cikin kwanaki 15 a jere
2020-02-19 10:10:38        cri
Hukumar lafiyar kasar Sin ta sanar a yau Laraba cewa, yawan sabbin mutanen dake kamuwa da cutar numfashi ta COVID-19 a wajen lardin Hubei inda cutar ta fi kamari ya ragu a cikin kwanaki 15 a jere.

A ranar Talata, sabbin mutanen da suka kamu da cutar a wajen lardin Hubei 56 ne, a bisa ga alkaluman da hukumar lafiyar ta fitar ya nuna cewa, ana samun raguwar yawan sabbin masu kamuwa da annobar ne cikin kwanaki 15 a jere wato tun daga ranar 3 ga watan Fabrairu.

Baki daya adadin sabbin mutanen da suka kamu da annobar cutar numfashi ta COVID-19 daga ranar 3 ga watan Fabrairu zuwa 18 ga wata kimanin 890 ne. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China