Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD ta nada Pang Sen dan kasar Sin a matsayin sabon jami'inta a kasar Namibia
2020-02-21 10:36:45        cri
Ofishin bunkasa cigaba na MDD ya bayyana Pang Sen dan kasar Sin a matsayin sabon jami'in ofishin a kasar Namibia, kakakin MDDr ya sanar da hakan a ranar Alhamis.

Haka zalika ofishin MDDr ya kuma sanar da nada madam Ingrid Macdonald 'yar kasar Australia a matsayin sabuwar jami'arsa a kasar Bosnia da Herzegovina, sai kuma Sezin Sinanoglou 'yar kasar Turkiyya a matsayin jami'arsa a kasar Tajikistan, a cewar Stephane Dujarric, mai Magana da yawun babban sakataren MDD Antonio Guterres.

Jami'in MDD ya ce ana fatan zasu daidaita ayyukan cigaba a tsakanin hukumomin MDD, da asusun gudanarwa da kuma shirye-shiryen MDD, wadanda suke da matukar muhimmanci wajen tallafawa kasashen don raya cigabansu nan da shekaru 10 don cimma nasarar shirin samar da dawwamamman cigaba na MDD.

Ya kara da cewa, zasu cigaba da tabbatar da daidaito tsakanin jinsi wajen zabar dukkan jami'an gudanarwar MDD, a kasashe da yankunan duniya 162.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China