Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban Namibia ya gana da Sun Chunlan
2019-11-08 20:12:28        cri
A yau Jumma'a, shugaban kasar Namibia Hage Geingob, ya gana da mataimakiyar firaministan kasar Sin Sun Chunlan a birnin Windhoek, fadar mulkin kasar Namibia.

A yayin ganawar tasu, Sun Chunlan ta bayyana cewa, kasar Sin tana son yin hadin gwiwa da kasar Namibia, wajen yin tattauna harkokin dake shafar moriyar kasashen biyu, da kuma zurfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu yadda ya kamata.

A nasa bangare kuma, Hage Geingob ya ce, kasar Sin muhimmiyar abokiyar kasar Namibia ce, kuma za ta dukufa wajen inganta shawarar "Ziri daya da hanya daya" cikin hadin gwiwarta da sauran kasashen Afirka, domin neman ci gaba cikin hadin gwiwa.

Har ila yau a dai wannan rana, Sun Chunlan ta halarci bikin "samar da haske" na kasar Namibia, domin jinjinawa likitocin kasar Sin, wadanda suka yi aikin jinyar cutar yanar ido kyauta, ga mutane kimanin dari 5 a kasar. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China