Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Namibia za ta dauki matakan farfado da tattalin arziki bayan da alkaluma sun nuna raguwar karfin sa
2019-12-09 10:38:38        cri
Minista a ma'aikatar kudin kasar Namibia Calle Schlettwein, ya ce mahukuntan kasar sun kuduri aniyar daukar managartan matakan raya tattalin arzikin kasar, bayan da cibiyar Moody mai bayyana alkaluman tattalin arziki ta tabbatar da koma baya da tattalin arzikin kasar ke fama da shi.

Mr. Schlettwein wanda ya bayyana hakan cikin wata sanarwa, ya ce da ma kasar na hasashen fuskantar wannan koma baya, duba da yanayin da tattalin arzikin kasar ke ciki, da ma yanayin koma baya na tattalin arzikin duniya da ake fuskanta.

Ministan ya ce tattalin arzikin Namibia ya gamu da koma baya a tsawon shekaru 2 da suka gabata. To sai dai kuma a hannu guda gwamnatin kasar, ta sha alwashin bijiro da matakai daban daban, wadanda za su kyautata yanayin da ake ciki a kasar, da karfafa gwiwar gudanar da hada hadar kasuwanci, da tabbatar da dorewar manufofin raya tattalin arzikin kasar, da kuma inganta tsarin bashi da gwamnati ke ta'ammali da shi.

Kaza lika gwamnati da hadin gwiwar sassa masu zaman kan su, ta fara aiwatar da matakan fadada ci gaban arzikin kasa, da kara yawan kasafin kudin kasar da kaso 42.2 bisa dari, a wani mataki na tallafar hidimomin raya tattalin arzikin kasar. (Saminu Alhassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China