Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaba Geinob ya lashe zaben shugaban kasar Namibia a wa'adi na biyu
2019-12-01 16:01:47        cri
Hukumar zabe ta kasar Namibia ECN, ta bayyana a jiya da dare cewa, Shugaban kasar mai ci, Hage Geinob, ya lashe zaben shugaban kasar a wa'adi na biyu na shekaru 5, da kaso 56.3 na kuri'un da aka kada, yayin da dan takarar Indipenda, Panduleni Itula ya samu kaso 29.2 na kuri'u.

Hage Geinob ya fuskanci takara mai zafi daga dan jam'iyyarsa ta SWAPO, wato Panduleni Itula, wanda ya tsaya takara a matsayin indipenda. Shugaba Geinob ya samu kuri'u 464,703 yayin da Panduleni Itula, ya samu kuri'u 242,657.

Hukumar ECN ta kuma sanar da jam'iyyar SWAPO mai mulki a matsayin wadda ta lashe kujerun majalisar dokoki. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China