Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban Namibia ya kaddamar da Kwalejin horar da sojoji da kasar Sin ta bada kudin ginawa
2019-10-18 10:14:27        cri

Shugaban Namibia, Hage Geingob, ya kaddamar da kwalejin horar da sojoji da kasar Sin ta bada kudin ginawa ta Namibia Command and Staff College, dake Okahandja, mai nisan kilomita 70 daga Windhoek, babban birnin kasar.

An kammala kwalejin da Sin ta taimaka wajen ginawa ne a shekarar 2016, kuma manufarta ita ce, inganta karfin kasar na horar da sojoji bisa dokokin aikin soja na kasar, da kuma rage yawan sojojin kasar da ba sa samun horo.

Da yake jawabi ga wakilai da manyan hafsoshin soji da suka halarci bikin kaddamar da kwalejin, Hage Geingob, ya bayyana kwalejin a matsayin cibiyar koli ta horar da sojoji ta kasar.

Shi ma a nasa jawabin, mukaddashin babban hafasan sojin saman kasar, Air Vice Marshal Martin Kapolo Pinehas, ya godewa gwamnatocin Sin da Namibia bisa samar da kudin kafa kwalejin.

Shi kuwa Jakadan Sin a kasar, Zhang Yiming, cewa ya yi, kwalejin za ta taka muhimmiyar rawa wajen samar da manya da matsakaitan hafsoshin soji, sannan za ta kasance tambarin abotar Sin da Namibia. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China