Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin da Namibia za su karfafa dangantaka karkashin dandalin FOCAC da BRI
2019-11-08 15:45:14        cri
Kasashen Namibia da Sin sun cimma matsayar karfafa dangantakar dake tsakaninsu karkashin dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afrika wato (FOCAC), da shawarar "ziri daya da hanya daya" (BRI), domin ciyar da dangantakarsu ta hadin kai bias manyan tsare-tsare a dukkan fannoni, mataimakiyar firaministar Sin dake ziyarar aiki Sun Chunlan ta bayyana hakan a ranar Alhamis.

Sun wanda ta gana da takwararta mataimakiyar firaministar Namibia kana ministar harkokin waje da huldar kasa da kasa ta kasar Netumbo Nandi-Ndaitwah.

A cewar Sun, shekara mai zuwa ne za'a cika shekaru 30 da kafuwar huldar diflomasiyya tsakanin Sin da Namibia, wanda hakan ke kara tabbatar da sabbin damammaki tsakanin bangarorin biyu. Ta ce kasar Sin a shirye take ta karfafa hadin gwiwar mutunta juna, da girmama matsayin siyasar juna a tsakaninta da kasar Namibia, domin amfanawa bangarorin biyu, da samun daidaito, da cin moriyar juna, da kuma aiwatar da muhimman yarjejeniyoyi da shugabannin kasashen biyu suka cimma matsaya kansu a ganawar da suka yi a shekarar bara.

Sun wacce ta yiwa mai masaukinta takaitaccen bayani game da muhimmin jawabin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar a lokacin bikin baje kolin kayayyakin da ake shigo da su kasar Sin karo na 2 a birnin Shanghai, tana mai cewa, gwamnatin Sin a shirye take ta hada gwiwa wajen gina tattalin arzikin duniya wanda ya dace da matsayin bude kofa, da kirkire kirkire, da yin musaya da sauran kasashen duniya.

Nandi-Ndaitwah, a nata bangaren ta ce, Namibia da Sin suna cin gajiyar dangantakar al'adu dake tsakaninsu, da yin musayar kwarewa ta fuskar ayyukan raya cigaban bangarorin biyu. A 'yan shekarun baya bayan nan, kyakkyawar dangantaka da hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu suna kara fadada, wanda hakan wani muhimmin al'amari ne wajen bunkasa shirin nan na raya cigaba mai dadadden tari mai taken "Harambee Prosperity Plan."

Ta ce Nambia tana matukar yabawa kasar Sin bisa yadda ta tsaya tsayin daka wajen zuba jari a kasar, kuma Namibia a shirye take ta koyi dabarun shugabanci mai salo irin na kasar Sin da kuma kara zurfafa hadin gwiwar dake tsakanin bangarorin biyu a fannonin raya ilmi, kiwon lafiya, samar da ayyukan yi, aikin gona, da samar da kayayyakin more rayuwa da sauransu, domin kawowa al'ummomin kasashen biyu alkhairai masu yawa. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China