Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Namibiya ta sanya hannu kan yarjejeniyar rancen filin gina tashar samar da lantarki bisa karfin iska
2019-12-30 15:37:16        cri
Ma'aikatar kula da muhalli da yawon bude ido ta kasar Namibiya, ta sanya hannu kan yarjejeniyar rancen filin da za a gina tashar samar da wutar lantarki da ya kai megawatt 44 da ake iya sabuntawa, wadda ake fatan zai taimakawa kasar samun wutar lantarki nata na kanta cikin shekaru biyar masu zuwa.

Ita dai wannan tasha mai amfani da karfin iska, wani bangare ne matakan da kasar ta ke dauka, don rage shigo da wutar lantarki daga waje, yayin da take kokarin samun makamashin da ake iya sabuntawa.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China