Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD ta yi tir da kisan ma'aikacin agaji a Sudan ta Kudu
2020-02-19 12:14:08        cri
Hukumar kula da ayyukan jin kai ta MDD, ta yi tir da kisan rashin imani da aka yi wa wani jami'in agaji a yankin Pibor na kasar Sudan ta kudu.

Cikin wata sanarwa da ya fitar jiya a Juba, shugaban ofishin hukumar a Sudan ta Kudu, Mathew Hollingworth, ya yi kakkausar suka kan kisan da aka yi wa jami'in, yana mai kira da a kama tare da hukunta wadanda ke da hannu.

Ya kuma yi kira ga gwamnati da dukkan masu ruwa da tsaki da al'ummomi a kasar, su kara zage damtse wajen kare jami'an agaji dake aiki ba tare da gajiya ba, domin bayar da taimakon da ake bukata da kuma inganta rayuwar mutanen dake rayuwa a kebantattun wurare. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China