2020-02-06 11:42:54 cri |
A cikin wata sanarwar da MDD ta fitar a ranar Laraba ta bayyana cewa, ana sa ran Guterres zai gabatar da jawabi a taron kolin na AU. Taken taron kolin wannan shekarar shi ne "Kawar da karar bindiga, samar da ingantaccen yanayin cigaban nahiyar Afrika."
Babban sakataen MDD zai yi wata ganawa da mambobin kasashen, kana zai halarci wasu taruka, daga bisani zai gabatar da jawabi a taron manema labarai a ranar 8 ga watan Fabrairu.
A lokacin da jami'in MDDr ya isa Habasha zai halarci wasu taruka don kammala cimma matsaya kan wasu batutuwan hadin gwiwa da AU, da suka hada da shirya babban taro game da batun daidaiton jinsi da bunkasa cigaban matan Afrika da kaddamar da shirin asusun shugabancin matan Afrika, a ranar 8 ga watan Fabrairu.
Sauran batutuwan kuma, sun hada da batun samar da damammakin raya cigaban tattalin arzikin Afrika ta hanyar albarkatun teku, wanda ya kunshi shirin hadin gwiwar nahiyar, wanda ake sa ran gudanarwa a matsayin wani muhimmin bangare a taron kolin na AU.(Ahmad Fagam)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China