Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wakilin Sin ya yi kira da a kiyaye kananan yara ta hanyar hana da kawo karshen rikici
2020-02-13 13:01:48        cri
Wakilin din din din na kasar Sin dake MDD Zhang Jun ya gabatar da jawabi jiya Laraba a babban taron tattauna batun kananan yara da rikicin karfin tuwo, inda ya yi kira da a kiyaye kananan yara ta hanyar hana da kuma daidaita rikicin karfin tuwo.

Zhang Jun ya ce, hanya daya tilo wajen kaucewa illata kananan yara daga rikice-rikice ita ce hana da daidaita rikicin karfin tuwo. Ya ce, ya kamata bangarori daban-daban su nace ga hanyar daidaita bambancin ra'ayi ta hanyar shawarwari da sulhuntawa cikin lumana, da kaucewa yin amfani ko barazanar yin amfani da karfin tuwo. Ya kamata a kara mai da hankali kan kandagarki, da kara kokarin ingiza aikin tabbatar da zaman lafiya tare da yin la'akari da bukatun kananan yara na musammam, ta yadda za a kiyaye kananan yara daga fadawa cikin rikici da tabbatar da hakkokinsu ciki har da na samun ilmi.

Ban da wannan kuma, Zhang Jun ya ce, daga shekarar 2018 zuwa yanzu, gwamnatin Sin ta samarwa Somaliya da Sudan ta kudu da Kongo Kinshasa da sauran kasashe tallafin kudi da fasahohi karkashin tsarin asusun tallafawa hadin kan kasashe masu tasowa, don taimaka musu wajen horar da jami'ansu da kara karfinsu, da matakan kiyaye kananan yara, kuma kwalliya ta biya kudin sabulu. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China