2020-02-11 09:46:30 cri |
Mataimakin sakatare janar na MDD kan ayyukan jin kai, Mark Lowcock, ya shaidawa manema labarai jiya a hedkwatar majalisar dake birnin New York cewa, barazanar farin a yankin kahon Afrika babban kalubale ne.
Ya ce akwai mutane miliyan 30 a kasashen da batun ya shafa, da suka hada da Habasha da Kenya da Somalia, wadanda kuma ke cikin tsananin rashin wadatar abinci. Yana mai cewa a yanzu, mutane miliyan 10 na wuraren da farin suka shiga.
Mark Lowcock, ya ce idan har ba a dauki mataki cikin makonni 3 zuwa 4 masu zuwa ba, za a fuskanci matsala mai tsananin gaske. (Fa'iza Mustapha)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China