Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin na samu ci gaba a yaki da cutar numfashi ta Corona
2020-02-13 13:25:04        cri
Wakilin dindindin na kasar Sin dake MDD Zhang Jun ya bayyana matakan da Sin take dauka na tinkarar cutar mumfashi a gun taron kwamitin raya al'ummar duniya da majalisar ta gudanar a jiya Laraba. Inda ya nuna cewa, matakan kandagarki da hana yaduwar cutar suna haifar da kyakkyawan sakamako, Sin na da imanin cimma nasara wajen tinkarar cutar da nasarar manfofin raya tattalin arziki da jin dadin jama'a kamar yadda aka tsara.

Zhang Jun ya kara da cewa, gwamnatin na mai hankali wajen tabbatar da tsaro da lafiyar jama'a yayin da ake fuskantar wannan cuta. Sin ta gina asibitoci guda biyu cikin kwanaki 10 a birnin Wuhan, wurin da ake fi fama da cutar, kuma ta tura ma'aikatan lafiya daga wurare daban-daban na kasar zuwa wuraren da ke fama da cutar da yawansu ya wuce dubu 20, ban da wannan kuma, ta bukaci hukumomi daban-daban da su bullo da sabbin magungunan yaki da cutar. Bayan namijin kokarin da aka yi, an samu ci gaba mai armashi.

Zhang ya jaddada cewa, tinkarar matsalar kiwon lafiya ta kasa da kasa kalubale ne na kasashen duniya baki daya. Sin na yi kira ga kasashen duniya da su ci gaba da hada kai da taimakawa juna, ta kuma yi kira ga al'ummar duniya da su mutunta shawarar WHO bisa tunanin da ya dace,

Jami'in na kasar Sin ya kara yin kira ga kasashen duniya da su kara amincewa da juna da kokarin raya makomar bai daya ga daukacin Bil Adama. Ya kuma nuna adawa da sanya batun siyasa kan batutuwan da suka shafi lafiyar jiki. A cewarsa, bai kamata kalamai na nuna bambancin wariya da wariyar launin fata su rika samun gindin zama ba. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China