![]() |
|
2020-02-19 10:50:44 cri |
Sanarwar ta kuma nemi a daidaita, da sa kaimi ga hanyar farfado da ayyuka, da tallafawa cinikin shige da fice da jarin ketare, kana kamfanoni daban-daban da su farfado da ayyukansu yadda ya kamata, har ma da sa kaimi ga manyan ayyuka dake da alaka da shawarar "ziri daya da hanya daya".
Dadin dadawa, sanarwar ta nuna cewa, kamata ya yi, a tafiyar da doka da shari'a, dangane da ciniki cikin gida, hadda dokar shigo da jarin ketare da sauransu, don baiwa kamfanoni masu jarin waje taimako na yin amfani da manufofi yadda ya kamata wajen tinkarar annoba. Sanann kuma, kamata ya yi a kafa tsarin magance annoba cikin sauri a ketare, don ba da taimako ga kamfanonin Sin dake ketare. (Amina Xu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China