Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Matsayin saukaka cinikayyar Sin yana daguwa
2019-12-11 20:14:04        cri

Wani sabon rahoton ya nuna cewa, a cikin 'yan shekarun da suka gabata, kasar Sin tana kara saukaka harkokin cinikayya a kai a kai.

A shekarar 2019, alkaluma suka nuna cewa, matsayin saukaka harkokin cinikayar kasar sun kai maki 76.93, adadin da ya karu da kaso 5.31 cikin dari idan aka kwatanta shi da na shekarar 2017, kana kamfanonin kasar Sin suna kara jin dadin yanayin cinikayya a kasar.

Yau cibiyar nazarin tsaro da saukaka cinikayya ta Re-Code ta birnin Beijing ta fitar da rahoton saukaka cinikayya na kasar Sin na shekarar 2020, inda aka bayyana cewa, ma'aunin da aka tsara kan gudanar da cinikayyar kasa da kasa a shekarar 2017 da sabon matakin da aka dauka wajen saukaka aikin binciken kwastam a shekarar 2018 sun taimaka matuka a bangaren saukaka cinikayya a kasar Sin.

Kwanan baya bankin duniya ya fitar da rahoton game da yanyin kasuwanci na shekarar 2020, inda aka bayyana cewa, yanayin kasuwancin kasar Sin ya kyautata matuka bayan da mahunkuntan kasar suka gudanar da kwaskwarima a wannan fanni (Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China