Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Cinikin wajen kasar Sin a shekarar 2019 ya karu da kaso 3.4
2020-01-14 13:29:07        cri

Alkaluman da hukumar kwastan ta kasar Sin ta fitar a yau Talata sun nuna cewa, cinikin wajen kasar a shekarar 2019 da ta gabata, ya kai Yuan triliyan 31.54, kwatankwacin dala triliyan 4.6, karuwar kaso 3.4 cikin 100.

Bugu da kari, darajar kayayyakin da kasar ta fitar zuwa ketare a shekarar da ta gabata, ta kai Yuan triliyan 17.23 karuwar kaso 5 cikin 100 a shekara guda, yayin da kayayyakin da ta shigo da su cikin kasar, sun kai Yuan triliyan 14.31, karuwar kaso 1.6, lamarin da ya haifar da rarar cinikin Yuan triliyan 2.92 wanda ya karu zuwa kaso 25.4 cikin 100.

Hukumar ta kuma bayyana cewa, adadin cinikayyar ketare da kayayyakin da aka shigo da su da wadanda aka fitar a shekarar 2019, duk sun kafa wani sabbin kambun bajinta. A bakin dayan shekarar kuma, cinikayyar ketaren kasar, ta ci gaba da karuwa a ko wane watanni hudu. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China