Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An yin cinikin dala biliyan 38.3 a ranar gwagware ta kasar Sin
2019-11-12 10:37:12        cri
Ranar gwagware ta kasar Sin ta samu tagomashi inda kantunan TMall suka yi cinikin yuan biliyan 268.4 kwatankwacin dala biliyna 38.3 a ranar Litinin.

A cewar Alibaba, mai manyan kantunan TMall, sama da kayayyakin kasashen waje 22,000 daga kasashen duniya da shiyyoyi 200 ne suka shiga hada hadar cinikin ta wannan shekara a kasar Sin.

Babban kamfanin cinikin ta intanet ya kaddamar da fara garabasar na shekara-shekara ta intanet ne a ranar 11 ga watan Nuwambar 2009, ranar da mafi yawan matasan Sinawa ke murnar bikin ranar gwagware ta kasar Sin. An zabi ranar ne saboda kamanceceniyar lambobin 11-11, wanda Sinawa ke mata lakabi da gwauro.

A lokacin farko na fara garabasar, kantunan na Tmall sun yi cinikin yuan miliyan 52. A bara kuma kamfanin na Alibaba ya yi cinikin yuan biliyan 213.5 a rana guda na garabasar. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China