Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Cinikin waje na Sin ya karu da kashi 2.4 a farkon watanni 11 na bana
2019-12-08 15:55:04        cri

Babbar hukumar kwastam ta kasar Sin (GAC), ta sanar da cewa, an samu karuwar cinikin waje a kasar a cikin farkon watanni 11 na shekarar nan ta 2019, inda ya karu da kashi 2.4 bisa 100 idan an kwatanta da makamancin lokacin bara.

Cikin wannan wa'adin, kwatankwacin yawan cinikin wajen kasar Sin ya kai yuan tiriliyan 28.5 kwatankwacin dala tiriliyan 4.14 .

Alkaluman sun nuna cewa, adadin kayayyakin da Sin ta fitar ketare ya karu da kashi 4.5 bisa 100 idan an kwatanta da makamancin lokacin bara wanda ya kai yuan tiriliyan 15.55, yayin da kayayyakin da kasar ta shigo da su ya kai yuan tiriliyan 12.95.

Gibin cinikin kasar ya karu da kashi 34.9 idan an kwatanta da makamancin lokacin bara wanda ya kai yuan tiriliyan 2.6.

Duk da koma bayan ci gaban harkokin kasuwanci da tattalin arzikin duniya, har yanzu cinikin wajen kasar Sin yana ci gaba da samun tagomashi a wannan shekarar, wannan ya nuna ingancin tattalin arzikin Sin, Li Kuiwen, daraktan sashen kididdiga na hukumar GAC ya bayyana hakan.

Huldar cinikin kasar Sin da EU da kuma ASEAN tana kara fadada, yayin da harkokin kasuwanci tsakanin kasashen dake kan shawarar ziri daya da hanya daya ke samun bunkasuwa cikin sauri.

Mu'amalar cinikayya tsakanin kasashen dake kan shawarar ziri daya da hanya daya ya karu da kashi 9.9 bisa 100 wanda ya kai yuan tiriliyan 8.35 daga watan Janairu zuwa Nuwamba, adadin da ya kai kashi 29.3 bisa dari dake cikin daukacin adadin cinikin wajen kasar.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China