Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An nemi a gaggauta shawarwari kan yarjejeniyar 'yancin ciniki tsakanin Sin da Japan da Koriya ta kudu
2019-12-23 13:40:14        cri
Jiya Lahadi, an yi taron ministocin harkokin ciniki da tattalin arziki na kasashen Sin da Japan da Koriya ta Kudu karo na 12 a birnin Beijing, inda ministocin uku sun sake jaddada cewa, ya kamata a kulla yarjejeniyar dangantakar hadin gwiwar tattalin arziki bisa dukkan fannoni ta yankin bisa lokacin da aka tsara a shekarar 2020, yayin da gaggauta yin shawarwari kan yarjejeniyar 'yancin ciniki na kasashen Sin da Japan da Koriya ta Kudu.

Haka kuma, bangarorin uku sun yi musayar ra'ayoyi kan dunkulewar tattalin arziki a yankin, da hadin gwiwar wurare, da kasuwanci ta yanar gizo da harkokin makamashi da dai sauransu, inda suka cimma matsayi daya kan manyan batutuwa, sannan sun shirya sosai ta fuskar tattalin arziki da cinikayya, dangane da taron shugabannin kasashen Sin da Japan da Koriya ta Kudu karo na 8 da za a yi.

Bugu da kari, yayin taron manema labarai da aka yi bayan taron, ministan harkokin kasuwanci na kasar Sin Zhong Shan ya bayyana cewa, a halin yanzu, ana fuskantar wasu kalubaloli a fannin tattalin arzikin duniya, wasu sun kuma nuna ra'ayin kariyar ciniki, ya kamata kasashen uku su karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu, domin kyautata hadin gwiwarsu a fannonin ciniki da zuba jari, ta yadda za su ba da gudummawa ga zaman lafiya, zaman karko da bunkasuwar kasa da kasa. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China