Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mutane 22 sun mutu a tirmitsitsi a kudu maso gabashin jamhuriyar Nijer
2020-02-18 10:21:37        cri

A kalla mutane 22 ne suka mutu a ranar Litinin sakamakon tirmitsistsi a yankin Diffa, dake shiyyar kudu maso gabashin jamhuriyar Nijer, kafafen yada labaran yankin sun bada rahoton.

A cewar gidan talabijin mai zaman kansa na Saraounia dake Nijer, lamarin ya faru ne da safiyar ranar Litinin a dakin taro na Matasa da Al'adu dake Diffa, a lokacin rabon kayayyakin abinci kyauta wanda gwamnan jahar Borno dake Najeriya, Babagana Oumara Zulum, ya gabatar a lokacin da ya ziyarci kasar Nijer.

Mafi yawan mutanen da suka mutu mata ne da kananan yara, a cewar rahoton.

Jahar Diffa tana kan iyakar Nijer da Naijeriya a shiyyar kudu maso gabashin jamhuriyar Nijer.

Tun a shekarar 2015, dubban 'yan gudun hijirar Najeriya sun tsallaka jahar Diffa sakamakon munanan hare haren ta'addanci na mayakan Boko Haram, wanda yayi sanadiyyar rayukan dubban fararen hula da jami'an sojoji a kasashen biyu. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China