Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An hallaka dakarun sojin Nijar 17 a kan iyakar kasar da Mali
2019-05-16 10:26:55        cri
Wata majiyar tsaron janhuriyar Nijar, ta ce a kalla sojojin kasar 17 ne suka rasu, kana wasu da dama suka jikkata, yayin wani kwantan bauna da wasu masu dauke da makamai suka yi musu, a wani wuri dake kusa da kan iyakar kasa da kasar Mali.

Majiyar ta ce an yiwa sojojin dirar mikiya ne a ranar Talata, a kusa da garin Tongo Tongo dake kan iyakar kasashen biyu. (Saminu Alhassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China