Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sojojin Najeriya sun ceto mutane 8 da aka yi garkuwa da su a arewa maso gabashin kasar
2019-11-18 09:09:36        cri
Sojoji sun ceto mutane 8 wadanda mayakan Boko Haram suka yi garkuwa da su a yankin Gwoza na jahar Borno dake shiyyar arewa maso gabashin Najeriya, kakakin rundunar sojojin kasar Aminu Iliyasu ya bayyana hakan a ranar Lahadi.

A wata sanarwa da aka baiwa kamfanin dillancin labarai na Xinhua a Legas, cibiyar kasuwancin Najeriyar, Iliyasu ya ce, dakarun sojojin sun fatattaki mayakan 'yan ta'adda na Boko Haram yayin arangamar da suka yi inda suka samu nasarar kubutar da mutanen 8 da suka hada da kananan yara 4 wadanda 'yan ta'addan suka yi garkuwa da su.

Kakakin rundunar sojojin ya ce, bayan an kubutar da mutanen, tawagar jami'an kiwon lafiya na rundunar sojojin ta baiwa kananan yaran alluran riga kafin cutar Polio.

Ya kara da cewa, ba'a samu mutuwa ko jikkatar jami'an sojojin ba a lokacin da suka yi arangama da mayakan.

A cewar kakakin, mayakan Boko Haram din sun tsere zuwa tsibirin Mandara da raunukan harbin bindiga. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China