2019-06-21 10:25:35 cri |
A cikin wata sanarwar da ministan tsaron kasar Niger Kalla Moutari ya gabatar a wannan rana, ya nuna cewa, sojojin bangarorin biyu sun harbi wadannan 'yan ta'adda 18 ne a wani matakin soji da suka dauka cikin hadin gwiwa daga ranar 8 zuwa 18 ga wata, a yankin Tongo-Tongo na jihar, inda kuma suka tsare wasu 'yan ta'adda 5 da kwato makamai masu dimbin yawa. Sanarwar ta ce babu wani sojan bangarorin biyu da ya rasa ransa ko ji rauni a aikin na wannan karon.
Yankin Tongo-Tongo na yammacin kasar Niger, na makwabtaka da kasar Mali a bangaren kudu maso gabas. Kuma kungiyoyi masu tsattsauran ra'ayi sun rika kai hare-hare a yammacin Niger, wuraren dake iyakokin Mali da Burkina Faso, lamarin da ya haddasa dimbin asara. (Amina Xu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China